Hotuna: Daga rayuwar kan titi zuwa lashe gasa a Birtaniya

0
255

Dauda Kavuma, mai shekara 37, ya shafe sama da shekara 10 yana koya wa yara 30 rawa

Yana zaune da su a gidansa da ke Kampala, babban birnin Uganda. Shekarun yaran nan sun bambanta daga uku zuwa 13.

Akasarin wadannan yaran marayu ne wasunsu kuma kawai haduwar titi ce. “Idan suka kira ni “Baba…Baba…Baba”, ina jin dadi.

Idan suka yi rawa, suna mancewa da matsalolinsu,” kamar yadda Kavuma David ya shaida wa TRT Afirka. “Ina koya musu yadda suke rawa da son juna.

Suna son junansu kamar ‘yan gida daya. Wannan ne karo na farko da muka yi gasa kuma wannan ce nasararmu ta farko,” in ji Mr. Kavuma.

Golden Buzzer gasa ce ta rawa wadda ake yi a duk shekara a Birtaniya. Gasar da aka yi a 2023 ita ce karo na 16, wadannan yaran da suka fito daga unguwar marasa galihu sun kai zagayen kusa da na karshe a gasar.

 

“Ana kiran sunan kungiyar mu Ghetto Kids kuma na hada wannan kungiyar ne domin bai wa wadannan yaran wata rayuwa ta biyu duk da cewa sun rasa iyalansu. Ina kokari domin ganin wadannan yaran sun yi karatu,” in ji Mista Kavuma.

A ranar Asabar, a lokacin da suka yi wasa a Birtaniya,’yan kallo da dama sun sha mamaki.

“Zama daya daga cikin dan kungiyar Ghetto Kids ya sa na samu dama daban-daban a rayuwa. Yana bani abinci da biya mani kudin makaranta da siya mani kaya.

“Idan daya daga cikinmu ba shi da lafiya, mu ma ba mu da lafiya haka kuma idan daya daga cikinmu na cikin farin ciki, mu ma muna ciki: in ji Ssegirinya Madwanah, daya daga cikin mamban Ghetto Kids inda yake bayani kan Kavuma bayan da suka kammala wasansu.

Kamar yadda gwamnatin Uganda ta bayyana, kimanin yara 15,000 ne wadanda ke tsakanin shekara bakwai zuwa 17 suke zaune kan titunan Kampala babban birnin Uganda.

Akasarin yaran nan sun fito ne daga lardin Karamoja da ke arewa maso gabashin Uganda. Sun guje wa rikici da rashin tsaro ne da ya addabe su.

“Duk da Mista Kavuma David ba mahaifinmu bane na asali, amma shi ke kula da mu. Godiya ga Daddy Kavuma, mun zo nan Landan. Mun zo nan mu yi wasa kuma za mu nuna wa duniya cewa a Uganda akwai yaran da suka iya rawa da zuciyoyinsu,” in ji Ssegirinya.

A lokacin da suka yi wasa a gaban alkalai, ‘yan kallo sun shiga wani irin shauki da suka ga shigowar Josephine Busingye, wata ‘yar rawa mai shekara biyar daga Ghetto Kids wadda ta zo da diyar roba a bayanta.

“Sunana Josephine kuma shekarata biyar,” kamar yadda Josephine Busingye ta shaida wa alkalai, kuma kowa a cikin ‘yan kallon sai ya tashi tsaye ya soma tafi.

“Za ka iya alfahari da kanka. Na ji dadi matuka – Zan ji dadi mu hadu a zagaye na gaba,” in ji Alkali Bruno Tonioli a wani bidiyo.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here