Ban da masaniya kan yi wa shugaban NIS Jere ritaya – Aregbesola

0
133

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, a ranar Laraba, ya musanta masaniya kan umarnin da aka bayar na yin murabus din mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa NIS, Isah Idris Jere, yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a fadar shugaban kasa, a karshen taron majalisar zartaswa na tarayya na mako-mako wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban kasa a Abuja, Ministan ya ce, “Banda wata masaniya.

In baku manta ba, mun rahoto muku cewa, Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa NIS, ta mika wa mukaddashin kwanturola Janar na Hukumar, Isah Idris takardar sanarwar ritaya daga ranar 24 ga Afrilu, 2023 ko kuma kafin ranan.

Takardar, mai kwanan wata 17 ga Afrilu, 2023, mai lamba CDCFIB/APPT.CG&DCG/61/VOL.IV/74 ta samu sa hannun Sakataren kula da Hukumar Kula da Ma’aikatar cikin gida, Obasi Edmond, bisa umarnin shugaban Hukumar kuma ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola.

An rubuta cewa, “Na rubuta ne domin in ja hankalinku game da cikar wa’adin shugabanci na shekara daya da Shugaban kasa ya ba ku ta takarda mai lamba. SH/COS/42/3/3/A128 kwanan wata Afrilu 22, 2022, kuma wanda wannan wa’adi zai kare ranar 24 ga Afrilu, 2023.

“Saboda haka, an umurce ka da ka mika ragamar shugabancin ga babban mataimakin Kwanturola-Janar yanzun ko kuma kafin ranar Litinin, 24 ga Afrilu, 2023, har zuwa lokacin da Shugaban kasa zai nada babban Kwanturola-Janar na Hukumar.

“Hukumar tana godiya a gare ku saboda gagarumar gudunmawar da kuke bayarwa ga Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya da kuma kasa, hukumar kuma tana yi muku fatan samun nasara a ayyukanku na gaba.”

Amma da aka nemi karin bayani kan wannan takarda, Aregbesola ya ce: “Baida wata masaniya kan batun” ‘It is Greek to me’ a turance.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here