INEC za ta bai wa Fintiri shaidar lashe zabe yau

0
115

A yau Laraba ne, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), za ta mika wa zababben gwamnan Jihar Adamawa, Ahmad Fintiri da maimakinsa shaidar lashe zabe.

INEC za ta mika masu shaidar ne, biyo bayan sake gudanar da zabukan da ba a kammala a daukacin fadin kasar nan.

Fintiri wanda ya kasance shi ne gwamnan jihar mai ci, INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben na gwamnan Jihar Adamawa tare da sunayen sauran ‘yan majalisar wakilai da kuma sanatoci .

Za a ba su shaidar ne da misalin karfe 11 na safiyar Labarba a shalkwatar Hukumar da ke Abuja.

Leadership ta ruwaito cewa, Fintiri dan takarar gwamna a PDP ya samu kuri’u 430,861, inda ya kayar da abokiyar takararsa ta jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Dahiru Binani wadda ta samu kuri’u 398,788.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here