Drogba ya caccaki Todd Boehly

0
124

Fitaccen tsohon dan wasan nan na Chelsea, Didier Drogba, ya caccaki daya daga cikin masu kulob din Todd Boehly kan irin matakan da yake dauka tun bayan sayensa daga Roman Abramovich.

Drogba na ganin cewa Chelsea ya kara sukurkucewa karkashin jagorancin Boehly inda ya yi ikirarin cewa Ba’amurken ya fi mayar da hankali kan matasan ‘yan wasa.

“Ba na gane kulob dina,” kamar yadda Drogba ya shaida wa Canal+. “Ba shi ne kulob din da na sani ba. Sabbin mutane da suka saye shi sun fito da sabon tsari. Eh, za mu iya kwatanta shi da abin da ya faru a lokacin [Roman] Abramovich inda aka rinka kawo ‘yan wasa da dama, amma matakai ne masu kyau.

“Kawo ‘yan wasa kamar Peter Cech da Andriy Shevchenko da Herman Crespo da Michael Essien da Didier Drogba da Florent Maloda da sauransu. An yi su ne domin cin kofi,” in ji Drogba.

“Akwai ‘yan wasa da suke da kwarewa. Amma dabarun da ake da su a yanzu na daban ne; muna kasada kan matasan ‘yan wasa. Amma wurin sauya tufafi na ‘yan wasa 30 ya gagari me hakkin kula ya kula da shi,” in ji shi.

Drogba ya ce kulob din ya rasa “jagorori masu kwarjini” wadanda za su iya shawo kan abubuwa masu wahala da kuma dora ‘yan wasa kan hanya madaidaiciya.

“Kana bukatar ‘yan wasa da za su kwace wasa, da za su yi aikinsu yadda ya kamata, kana bukatar ‘yan wasa da za su kawo dan karamin hauka a filin wasa,” in ji shi.

Kulob din yana dai shan caccaka kan yadda wasaninsa ke tafiya a wannan kaka. Yanzu haka shi ne na 11 a teburin gasar Firimiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here