WAFU B U-20: An fitar da jadawalin kasashen da za su fafata da Najeriya

0
172

Tawagar kwallon kafar mata ta Nijeriya, the Falconets, za ta fafata da takwarorinta na Jamhuriyar Nijar, Togo da Burkina Faso a Rukunin B na Gasar cin Kofin Mata ‘yan kasa da shekara 20 na Kasashen Yammacin Afirka.

An fitar da jadawalin ne ranar Litinin a hedikwatar WAFU-B da ke Abidjan, babban birnin Ivory Coast.

Za a gudanar da gasar daga ranar 20 ga watan Mayu zuwa 4 ga watan Yuni na 2023, a birnin Kumasi na kasar Ghana.

Wannan ne karon farko da za a gudanar da irin wannan gasa mai suna WAFU B U-20 Girl’s Championship.

Mai masaukin baki Ghana, za ta fafata da Benin da Cote D’Ivoire a Rukunin A.

A bangaren maza, tawagar kwallon kafar Nijeriya ta Flying Eagles za ta barje gumi da takwarorinta na Benin da Togo a Rukunin B, yayin da tawagar Ghana ta Black Satellites za ta hadu da Cote d’Ivoire.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here