Gwamnatin tarayya ta amince da fara amfani da allurar riga-kafin zazzabin Maleriya

0
140

Gwamnatin tarayya ta amince da fara amfani da allurar riga-kafin zazzabin Maleriya wanda Jamiā€™ar Oxford da ke Birtaniya ta samar.

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa NAFDAC ce ta ba da izinin amfanin da riga-kafin duk da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sauransu ba su kammala bincike kan rashin hadarinsa ga dan Adam ba.

Da haka Najeriya ta zama kasa ta biyu a nahiyar Afirka da ta amince da riga-kafin, bayan kasar Ghana.

Rahoton WHO ya nuna a shekarar 2021 Najeriya ce kasar da ke dauke da kashi 27% na masu maleriya da kuma kashi 32% na wadanda ta yi sanadin mutuwarsu a duniya.

A ganinka samar da allurar rigakafi shine zai kawar da zazzabin a Nigeriya?

Wacce hanya kuke ganin ya kamata abi wajen kawar da Maleriya a kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here