Osimhen yayi biris da tayin manyan kungiyoyin Turai

0
177

Dan wasan gaba na Napoli Victor Osimhen ya ce zai cigaba da zama a kungiyar ta sa, duk da cewar an shafe lokaci mai tsawo ana alakanta da shi da sauya sheka zuwa wasu manyan kungiyoyin nahiyar Turai, cikinsu har da Manchester United da kuma Chelsea.

Yanzu haka dai Osimhen na daga cikin ‘yan wasan gaba da ke kan gaba a duniyar tamaula, wanda a bana kadai ya zura kwallaye 25 a wasanni 30 da ya buga.

Dan wasan ya taimaka wa Napoli darewa jagorancin gasar Seria A da tazarar maki 17, yayin da kuma kwallayensa suka yi tasiri a kaiwa zagayen wasan kwata final na gasar Zakarun Turai da kuniyar tasa ta yi.

Baya ga United da Chelsea, sauran kungiyoyin da ke  neman kulla yarjejeniya da wasan na Najeriya, sun hada da Bayern Munich da kuma PSG.

Sai dai yayi wata ganawa da manema labarai, Osimhen ya ce yana nan daram a kungiyarsa, domin tuni tana cikin manyan kungiyoyin Turai, don haka babu bukatar neman sauyen sheka a halin yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here