‘Yan bindiga sun kashe mutum 30, sun banka wa gidaje wuta a jihar Kaduna

0
134

A wani sabon harin da ‘yan bindiga suka kai a kauyen Runji da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna sun kashe a kalla mutum 30 tare da cinna wuta ga gidaje da dama. 

 

Sabon harin wanda ya wakana wajajen karfe 10 na daren ranar Asabar na zuwa ne kasa da kwanaki uku da ‘yan bindigan suka kashe mutum takwas a kauyen Atak’Njei dukka a karamar hukumar ta Zangon Kataf din.

LEADERSHIP ta tattaro daga majiyoyinta cewa ‘yan tsaron sa-kai da ke yankin sun yi kukan kura suka tunkari maharan daga bisani kuma sojoji suka kawo musu dauki domin fatattakar masu kai harin.

Mazauna kauyen sun gode da yadda sojojin suka yi gaggawar kawo dauki tare da cewa da ba din hakan ba da ‘yan bindigan sun share kauyen dukka.

 

Kwamishinan kula da tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar harin, yana mai cewa gwamna Nasir El-rufai ya yi tir da harin da ya janyo mutuwar mutane da dama.

 

Ya ce, rahotonnin da sojoji suka ba su ya yi nuni da cewa wasu da dama kuma an jikkata su tare da Kona wasu gidaje da dama a harin.

 

Ya ce a daidai lokacin da gwamnan ke zama jiran cikakken rahoton harin, ya yi tir da Allah wadai da wannan lamarin.

 

“Gwamnan ya Mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu tare da addu’ar Allah musu rahama, wadanda suka jikkata Kuma Allah ba su lafiya.”

 

Ya nemi jama’a su cigaba da yin hadin kai da jami’an tsaro domin dakile bata-gari tare da nanata aniyar Gwamnatin na yin duk Mai yiyuwa wajen dakile ‘yan ta’adda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here