Tambuwal ya ci zaben Sanata

0
132

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya lashe zaben Sanatan Sakkwato ta Kudu.

Tambuwal na Jam’iyyar PDP ya kai bantensa ne bayan da ya doke Sanata mai ci, Ibrahim Danbaba na APC.

Tambuwal ya lashe zaben da kuri’u 100,860 a yayin da Sanata Danbaba ya samu 95,884.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here