Kylian Mbappe ya kafa sabon tarihi a Paris Saint Germain

0
184

Kylian Mbappe ya kasance dan wasan da ya fi ci wa Paris St-Germain kwallo a Gasar Ligue 1 bayan sun doke Lens da ci 3-1 ranar Asabar.

Hakan ya sa sun zama na daya a saman tebirin gasar da maki biyar.

Mbappe, wanda ya zura jimillar kwallo 139 a wasan lig 169 da ya yi wa kulob din, yanzu ya zarta adadin kwallon da Edinson Cavani ya ci.

Mbappe da Lionel Messi da kuma Vitinha ne suka ci wa PSG kwallo, yayin da Przemyslaw Frankowski ya ci wa Lens tata kwallon ta hanyar bugun fenareti.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here