INEC na kammala zabukan gwamnoni da ‘yan majalisun dokoki

0
132

A ranar Asabar din nan ne hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya, INEC, take gudanar da zabukan da ba a kammala ba a watan jiya.

Za a yi zabukan ne a jihohin Adamawa da Kebbi da ke arewacin kasar.

Sai dai zaben jihar Adamawa ya fi daukar hankali inda ake fafatawa tsakanin gwamna mai-ci Ahmed Fintiri na jam’iyyar PDP da Sanata Aisha Binani, ta jam’iyyar APC.

Kazalika za a kammala zabukan kujeru biyar na ‘yan majalisar dattawa a jihohin Kebbi da Sokoto da kuma Zamfara.

INEC za ta karkare zabukan kujerun ‘yan majalisun tarayya 31, sai dai wanda ya fi jan hankali shi ne na Doguwa/Tudunwada a jihar Kano inda shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin tarayya Alhassan Ado Doguwa ke neman yin ta-zarce.

Haka kuma hukumar INEC za ta kammala zabukan kujeru 58 na ‘yan majalisun dokokin jihohi.

‘Ba yaki ba ne’

Hukumar zaben ta Nijeriya ta ce ta kammala raba kayan aiki kuma tana sa ran dimbin masu zabe ne za su fito domin jefa kuri’unsu.

Kakakin INEC, Festus Okoye, a wata sanarwa da ya fitar ya roki ‘yan siyasa su kalli zaben a matsayin wata dama ta tabbatar da ‘yancinsu ba a matsayin “yaki” ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here