Yadda Real Madrid ta casa Chelsea a gasar Zakarun Turai

0
177

A ranar Laraba da daddare ne Real Madrid ta doke Chelsea da ci biyu da nema a wasan kusa da na karshe na cin Kofin Zakarun Turai, UEFA, a filin wasa na Santiago Bernebeu.

Karim Benzema, fitaccen dan wasan gaba na Madrid shi ya jagoranci casa Chelsea, da kwallon farko a minti na 21 da fara wasan.

Da cin kwallon nasa, Benzema ya ruga a guje wurin abokinsa Vinicius Jr, suka taya juna murnar samun nasara. Da ma dai shi Vini din ne ya fara harba kwallon a ragar Chelsea, amma mai tsaron ragar Kepa ya koro ta waje.

Alamu sun nuna tun a zagayen farko alkadarin Chelsea ya karye, amma hakan bai bayyana karara ba sai da aka sallami dan wasanta Ben Chilwell.

Minti 14 da dawowa daga hutu, sai alkalin wasa ya daga wa dan wasan tsakiya na Chelsea, Ben Chilwell jan kati, bayan ya cafko kafadar dan wasan Madrid, Rodrygo har ya kai shi kasa, dab da ragar Chelsea.

Korar Chilwell ta haifar da gibi a tawagar ta kociya Frank Lampard, wanda ya karbi ragamar jagorantar Chelsea a makon jiya. Haka dai wasa ya ci gaba Chelsea da ‘yan wasa 10 kacal.

A minti 71 na wasan, Manajan Real Madrid, Carlo Ancelotti ya fara sauya ‘yan wasansa, inda ya cire matashin dan wasan gaba nan mai tilon suna dan asalin Brazil, wato Rodrygo.

Cikin minti uku da maye gurbin Rodrygo, Marco Asensio bai jira jininsa ya gama tsinkewa ba, sai ya durma kwallo ta biyu a ragar Chelsea. A wannan karon ma dan wasa Vinicius ne ya taimaka aka ci kwallon.

Hakan ya kwantar da hankalin masoya Madrid har dai aka tashi wasa Madrid na da kwallo biyu, Chelsea tana nema.

Da ma dai Real Madrid shi ke rike da Kofin UEFA, baya ga cewa shi kadai ne kulob din da ya taba lashe gasar sau 14.

Masu sharhi kan wasanni sun koka da kociyan Chelsea saboda benca mai tsaron raga dan asalin Senegal, Edouard Mendy, inda ya zabi saka mai tsaron ragar da aka dade da canfawa a gasar Zakarun Turai, wato Kepa Arrizabalaga.

Sai dai kuma, da aka tambayi Lampard game da yadda ta kaya a wasan nasu da Madrid, ya nace cewa bai fid da rai ba cewa Chelsea za ta shawo kan wannan cikas idan Madrid ta je Stamford Bridge.

Jaridar The Irish Times ta ambato Lampard yana ayyana fatan nasara a wasan na gaba, yana cewa, “Babban kalubale ne tunkarar hazikin kulob kamar Real Madrid, amma har yanzu muna iya samun nasara.”

Yayin da za a jira mako mai zuwa don buga zango na biyu na wasanta da Chelsea, Real Madrid tana cike da fatan kai wa ga gaci, na buga wasan dab da na karshe, don neman cin Kofin a karo na 15.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here