Babu sunan Abba a jerin sunayen ’yan takarar Jihar Kano da NNPP ta tura wa INEC – APC

0
173

Jam’iyyar APC ta garzaya kotun inda take kalubalantar sakamakon zaben Gwamnan Jihar Kano, wanda Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya lashe.

APC ta shaida wa kotun sauraron Kararrin Zaben Gwamnan Kano cewa, hasali ma, Abba Kabir, bai cancanci tsayawa takara a zaben ba.

Takardar karar da ta shigar ta bayyana cewa babu sunan Abba a jerin sunayen ’yan takarar Jihar Kano da NNPP ta tura wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here