Kotu ta sake aike wa Rarara sammaci saboda taurin bashi

0
188

Wata babbar kotun shari’ar addinin Musulunci da ke Kano ta yi umarnin a sake rubuta wa mawaki Dauda Adamu Kahutu (Rarara) sabuwar takardar sammaci saboda kin halartar zamanta da ya yi.

Kotun, wacce ke zamanta a unguwar Rijiyar Zaki da ke birnin Kano, karkashin Mai Shari’a Halhalatul Khuza’i Zakariyya, ce ta bayar da umarnin yayin zamanta na ranar Talata.

Ana karar Rarara ne kan kin biyan wasu kudaden wasu wayoyin salula da yake karba yana raba wa mutane daga hannun wani dan kasuwa mai suna Muhammad Ma’aji.

Yawan kudin dai ya kai kimanin Naira miliyan goma da dubu dari uku.

Lauyan mai kara, Barista I. Imam, ya shaida wa kotun cewa, wanda ake karar bai mutunta sammacin da aka kai masa ba saboda kin halartar zaman kotun.

Lauyan ya roki kotun da ta bayar da umarnin a kamo Rarara kasancewar ya raina ta.

Sai dai ya kara da cewa bai san ko sammacin da aka rubuta wa wanda ake karar da farko ya isa gare shi ba, ko kuma a’a.

Kotun ta tambayi jami’inta da ya kai sammacin, Isma’il Zuhudu, ko ya ba Rarara hannu da hannu, inda ya ce ya lika masa takardar a kofar gidansa kamar yadda kotun ta yi umarni, saboda sun neme shi don ya ba shi hannu da hannu amma bai same shi ba.

Mai Shari’a Halhalatul Khuza’i Zakariyya ya ce kasancewar wanda ake tuhuma bai zo ba kuma bai aiko ba, kotun ta yi masa uzuri saboda wannan ne karo na farko da ya yi haka.

Daga nan ne ya ba da umarnin a sake rubuta sabon sammaci ga Rarara a mika masa hannu da hannu ko kuma a like masa a kofar gidansa da ke kan Titin Gidan Zoo da ke Kano tare da wallafa sammacin a shafukan sada zumunta da kafafen yada labarai.

Kotun ta sanya ranar Alhamis, 13 ga watan Afrilu, 2023 domin ci gaba da sauraron karar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here