Mahaifin Messi ya gana da shugaban Barcelona

0
239

Mahaifin Lionel Messi wanda shi ne manajansa, Jorge, ya gana da shugaban Barcelona, Joan Laporta, kan yiwuwar komawar dan wasan PSG tsohuwar kungiyarsa.

Jaridar Mirror ta Birtaniya ta ruwato cewar duk da cewar Barca na son Messi ya koma, kungiyar ba ta bai wa Messi kwantiragi ba tukunna.

Babu tabbas kan makomar Messi a PSG domin kungiyar ta dakatar da maganar sabunta kwantiraginsa.

Messi ya zura kwallo 19 a raga yayin da ya taimaka wajen zura kwallo 20 a kakar bana kuma ya nuna farin cikinsa na kasancewa a kulob din yayin da yake kokarin sabawa da rayuwa a Faransa.

An yi wa Messi ihu a wasan da PSG ta buga da Lyon a makon jiya, lamarin da ya nuna akwai rashin jituwa tsakanin dan wasan da magoya bayan kulob din.

Wannnan rashin tabbas na zuwa ne a daidai lokacin da Barca ta tabbatar da cewar an yi tuntuba tsakaninta da dan wasan.

A watan jiya mahaifin Messi ya je Saudiyya inda aka yi ta rade-radin cewar ya je ne saboda dansa zai koma murza leda a can.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here