Abu bakwai kan wasan Bayern da City a Champions League

0
153

Manchester City za ta karbi bakuncin Bayern Munich a wasan farko zagayen quarter finals a Champions League ranar Talata a Etihad.

City ce ke rike da Premier League na bara, wadda take mataki na biyu da tazarar maki shida tsakaninta da Arsenal ta daya.

Bayern ita ce ta daya a teburin Bundesliga, mai rike da kofin babbar gasar tamaula ta Jamus na bara.

City ta kawo wannan matakin bayan da ta fitar da RB Leipzig, ita kuwa Bayern ita ce ta yi waje da Paris St Germain.

Sai dai City ta ci wasa 10 a jere a gida a kan kungiyoyin Jamus a Champions League da cin kwallo 39 -10.

3. Ba a ci kungiyoyin biyu kwallaye da yawa ba a Champions League:

Kwallo biyu ne ya shiga ragar Bayern, yayin da uku aka zura wa City a raga a bana a Champions League.

Wasa bakwai Bayern ta yi kwallo bai shiga ragarta ba, a karawa da Viktoria Plzen ne Bayern ta yi nasara da cin 4-2, sune biyun da aka zura mata a raga.

4. Watakila Muller ya kafa tarihi a Champions League:

A wasan da Bayern ta doke Paris St Germain a karawa ta biyu zagayen ‘yan 16, karo na 99 da aka yi nasara da Thomas Muller a Bayern Munich daga wasa 140.

Zai zama na uku da aka ci wasa 100 da shi a Champions League, bayan Cristiano Ronaldo mai 115 a Manchester United da Real Madrid da kuma Juventus.

Sai kuma na biyu Iker Casillas mai 101 a Real Madrid da Porto.

Sai dai Muller zai kafa nasa tarihin a kungiya daya Bayern Munich.

5. Wasan farko da Tuchel zai ja ragamar Bayern a Champions League:

Thomas Tuchel, mai shekara 49 ya lashe Champions League a Chelsea, kenan ya san dadin kofin da ya dauka bayan cin City 1-0 a wasan karshe.

Wasa na uku baya da ya fuskanci Pep Guardiola kenan.

Tuchel a Chelsea ya ci City 1-0 a FA Cup daf da karshe a Afirilun 2021, Tuchel ya yi rashin nasara a Borussia Dortmund a 2016 a DFB Cup karawar karshe a bugun fenariti a hannun Guradiola a Bayern, bayan da suka tashi 0-0 a minti 120.

6. Na daya a cin kwallaye da na farko a yawan bayarwa a zura a raga:

Erling Haaland ya ci wa Man City kwallo 10 a Champions League a kakar nan.

Ba bako bane wajen cin kwallaye a gasar, wanda ya zura 33 a wasan farko 25 da ya yi a gasar.

Wato yana da tazarar 13 ga duk dan wasan da ya ci kwallo a karawa 25 a farkon fara Champions League.

Bayern tana da ‘yan wasa biyu da ke kan gaba a bayar da kwallo a zura a raga a bana da ya hada da Joao Cancelo mai wasan aro daga City, wanda ya bayar da biyar.

Na biyu kuwa shine Leon Goretzka wanda ya bayar da hudu aka zura a raga.

7. Karawa ta zakarun lik din kasashensu:

Bayern da Man City daya ne daga wasa hudu a zagayen quarter finals tsakanin masu rike da kofin lik din kasarsu.

Bayern Munich tana da Champions League shida, ita kuwa City ba ta taba lashe kofin ba, duk da Guardiola yana da biyu a Barcelona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here