An bai wa masallatai 15 izinin yin sallar tahajjud a Diffa

0
147

Hukumomin jihar Diffa ta jamhuriyar Nijar sun bai wa masallatai 15 izinin gudanar da sallar tahajjud.

A wata sanarwa da hukumomin jihar suka fitar sun bai wa masallatan 15 damar buɗewa cikin dare domin gudanar da sallolin ƙiyamul-laili da mafi yawan masallatai ke farawa cikin daren yau.

Wannan dai shi ne karo na biyu tun bayan da jihar ta faɗa ƙarƙashin dokar ta-ɓaci a shekarar 2015.

Mazauna jihar na nuna jin daɗin ganin yadda suka ce a shekarar da ta gabata masallatai 10 ne aka buɗe, duba da yadda hukumomin ke ƙoƙari wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro, wanda hakan ya sa a bana aka buɗe masallatai 15, domin gudanar da ibadar.

Sai dai sun yi kira ga hukumomin da su duba yiwuwar barin babura masu kafa uku – da aka fi amfani da su wajen sufuri a kasar – a yi aiki da su a lokacin tafiya massallatai domin sauƙaƙa musu wahalar zirga-zirga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here