An sako tsohon mataimakin gwamnan Nasarawa da aka yi garkuwa da shi

0
104

Yan bindiga sun sako tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa, Farfesa Onje Gye-Wado wanda suka yi garkuwa da shi.

Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindigar sun sako shi ne kafin wayewar garin Litinin bayan sun karbi kudin fansa daga hannun iyalansa.

A ranar Alhamis ne ’yan bindiga suka kutsa gidan Farfesa Gye-Wado da karfin tsiya suka yi awon gaba da shi.

Daga baya suka bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan saba’in, amma iyalansa suka yi ta tattaunawa da su tare da neman ragi.

Wani daga cikin iyalansa ya bayyana cewa kudin fansar da aka biya ya kusa Naira miliyan hudu.

Ya ce ’yan bindigar “sun karbi kudin fansar ne da kuma katin waya na Naira dari biyu ne a kusa da Makarantar Sakandaren Dutsen Mada kafin daga baya suka sako shi daga maboyarsa da ke kusa da Tsaunin Mada da Nasarawa Eggon.”

Daga nan ne aka wuce da shi zuwa Fadar basaraken Wamba, Oriye Rindre, Mai Shari’a Lawal Musa Nagogo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here