Abin da ya sa muka dage mukabala da Dakta Idris bisa kalamansa a kan manzon Allah – Hukumar Shari’a

0
107

Hukumar Shari’ar Musulunci ta jihar Bauchi ta dage zaman tattaunawa da ta shirya a tsakaninta da malamai da kuma Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi bisa wani furuci da ya yi na cewa ‘Ko taimakon Manzon Allah ma ba su so’ furucin da ya janyo zafafan muhawara a cikin garin ta Bauchi da ke waye da ake ganin kamar malamai bai yi amfani da lafuza masu kyau ba ga Manzon Allah.

Ita dai hukumar Shari’a ta zargi Malam Idris da yin amfani da kalmar da ya kasance na kasanci ga Manzon da munanawa tare da rashin ladabi, don haka ne ta shirya zama da shi domin ankarar da shi wannan kuskuren.

Idan za a tuna dai hukumar ta ware yau Asabar 8 ga watan Afrilu domin yin wannan zaman amma daga bisani aka ga ta dage zuwa wani lokacin da ba a sanar ba zuwa yanzu.

Malam Mustapha Baba Ilaleh, shugaban hukumar shari’ar Musulunci ta jihar Bauchi ya shaida ta cikin hirarsa da wata gidan rediyo cewa, nan ba da jimawa ba za su sake sanar da sabon ranar da za a yi wannan zaman.

Ya ke cewa: “Lallai mun shirya za a yi zama da Malam Idris Abdul’aziz dangane da wasu kalmomi da ya fada; to kalmar karshe da ya furta sai ya zama ya yi wa al’ummar musulmai zafi musamman wadanda suka kasance masoyan Manzon Allah (SAW). To wannan kalmar ya daga hankali sosai a ciki da wajen gari. Hakan ya sa aka kira zama na musamman da shi aka kuma tanadi malamai domin a zo a zauna a tattauna da shi a ankarar da shi munanan kalma da ya ambata ko dai a yarda da muninsu don babu maganar kariya a wannan kalmar domin kalmomi ne wadanda da wuya su dauki wani tawili.

“Wannan ya sanya muka yi shirye-shirye domin a yi a ranar Asabar 8 ga watan Afrilu amma sakamakon wasu abubuwa da muka ga ya dace mu kammala su mu tanadasu ya sa muka ga ya dace mu daga daga baya za a yi wannan zaman.”

“Shi wannan zaman mun shirya shi ne sakamakon wata ibara wato wata jimla da shi Malam Idris ya fada lokacin da yake kokarin kore istigasa da istina neman taimako ko neman agaji ba a yi a wajen kowa sai Allah (SWT), ya ce, baya nema a wajen Inyasi, ba ya nemi a wajen Tijjani ba ya nema a wajen Abdulkadiri ba ya nema a wajen Shehu Danfodio sai ya ce kai ko (Wa’izabilla) ko Manzon Allah ma ba mu neman taimako a wajensa, ‘ko Manzon Allah ma ba mu bukatar taimakonsa’, wa’iyazubillah.

“To ka ga wannan wata jimlace da ba za ta dauki wani tawili ba. Malamai suke fassara wannan jimlar da cewa akwai ihana ga Annabi (SAW) wato akwai kaskantawa ga Annabi (SAW) kuma akwai abun da ake kira ‘su’ul’adabi’ wadannan suka sabbaba muka ga ya kamata a nemeshi ya zo ya yi bayani tattare da wannan jimlar tasa ta karshe don mu a kanta muke magana. Da kuma munanta ladabi wadanda bai kamata ya fadi wadannan kalmomin ba.”

Malam Mustapha Ilaleh ya karyata batun da ke cewa sun dage zaman ne sakamakon janyewa da kungiyar Izalah ta yi a wajen zaman, ya ce sam ba wannan ne dalilin da ya janyo dage zaman ba domin tun kafin kungiyar ta aiko da wasikarta sun riga ma sun cimma matsayar dage zaman.

Ya ce, makasudin shirya zaman shi ne domin a tabbatar da yin gaskiya da fito da batutuwa daga littafai na magabata.

Daga nan Baba Ilaleh ya yi kira ga al’umma da a kowani lokaci suke amsar tacaccen ilimi sannan jama’a su kara sanin hakkokin Manzon Allah (SAW) don a so shi so ta gaskiya ta hakika a bi shi bi ta sunnar gaske ba ta riyawa a baki ba kawai.

A cewarsa, akwai bukatar a kullum a ke amfani da hujja mai karfi da hujja mai asali tare da bin fassara da ma’anoni kamar yadda magabata suka bayar a sullisi na Kur’ani ko hadisai.

Daga nan ya jawo hankalin jama’a da cewa koda irin wannan abun ya faru kada su dauki doka a hannunsu kuma kada su furta kalamai marasa kan gado domin ya bada tabbacin cewa za su bi lamarin kuma za a fito da hakikanin abubuwan da suka dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here