Dalilan ɗage muhawara da Sheikh Idris ‘kan zargin munana kalamai’ – Hukumar Shari’a

0
126

Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi ta yi ƙarin haske a kan dalilanta na ɗage zaman tattaunawa da ta shirya da Sheikh Idris Abdul’aziz, wanda ake zargi da munana kalamai a kan Annabi Muhammadu.

Tun farko a yau Asabar ne, hukumar ta shirya gudanar da muhawara da malamin addinin Musuluncin, sai dai sa’o’i kafin lokacin sai ga wata sanarwa da ke cewa an ɗage zaman.

Ana zargin fitaccen malamin ne da furta kalamin cewa ‘ba ya buƙatar taimakon Annabi’, abin da mafi yawan mutane ke gani, munana lafazi ne ga Fiyayyen Halitta.

Lamarin ya janyo muhawara mai zafi da ka-ce-na-ce har a tsakanin malaman addinin Musulunci da ke arewacin Najeriya, inda wasu suka fara kiraye-kirayen lallai hukumomi su ɗauki mataki.

Mustafa Baba Illelah, shugaban Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi ya ce abin da ya sa suka ɗage zaman shi ne a bayar da dama ga malamin, da kuma sauran malaman da za su yi muhawarar, har ma da hukumomi duk su shirya.

“Duk lokacin da ake so za a yi wani zama, da wani malami domin a tuntuɓe shi bisa ga bayanan da ya yi, ana buƙatar ka yi wani tsari na musamma na yadda za ka ba wa mutum dama ya faɗi haƙiƙanin abin da yake nufi,” in ji Mallam Mustafa.

Ya ce matakin kuma zai ba da damar “A samu malamai sanannu kuma ƙwararru a fannin da ake magana a kai, to wannan ya sababba, lokacin da aka sa, a kan yau za a yi, da sauran shirye-shirye da kuma wasu dalilai, suka sa muka ga dacewar a ɗaga zuwa wani lokaci “.

A cewar Mallam Mustafa, komai yana buƙatar tsari, yadda za a tsara wurin da za a yi zaman. “Yana da kyau mu samar da irin abubuwan da ake buƙata, don wanda za a yi irin wannan zaman da shi.”

‘Ba zama irin na titi ba ne’

Mallam Mustafa Baba Illelah ya nanata cewa ba don Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi suka ɗage zaman a ranar Asabar ɗin nan ba. Sun yi hakan ne don kowanne ɓangare ya shirya.

Zama ne da ke buƙatar a yi tsari da ba da tsaro ga kowanne ɓangare, in ji Mallam Mustafa Baba Illelah. “Ba zama ne kawai da za a je, a yi kamar a bakin titi ba”.

Akwai buƙatar mu ba shi tsari. Mu ba shi kariya, a cewar shugaban hukumar shari’ar ta Bauchi.

Haka zalika, su ma malaman sai an tanadi wurin da zai ba da damar a ba su tsaro da kariya don gudanar da zaman cikin kwanciyar hankali, ya ƙara da cewa.

A ranar 10 ga watan Yulin shekara ta 2021, gwamnatin Kano ta shirya irin wannan muƙabala da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a jihar.

An dai zargi malamin na Kano ne da furta kalaman saɓo a kan Annabi Muhammadu (SAW), abin da ya janyo daga bisani aka gurfanar da shi a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here