Lampard ya zama sabon kocin Chelsea

0
121

Frank Lampard ya zama kocin Chelsea na rikon kwarya zuwa karshen kakar wasanni ta bana, bayan shekara biyu da korarsa.

Tsohon dan wasan Chelsea ya horar da kungiyar tsakanin Yulin 2019 zuwa Janairun 2021, wanda Thomas Tuchel ya maye gurbinsa.

Ranar Lahadi Chelsea ta sallami Graham Potter, wanda ya maye gurbin Tuchel a Stamford Bridge.

Chelsea tana mataki na 11 a teburin gasar Firimiya, bayan yin kunnen doki da Liverpool a ranar Talata.

Bruno Saltor ne ya ja ragamar Chelsea a karawar – Lampard, mai shekara 44 ya kalli wasan na hamayya a ranar a Stamford Bridge.

Chelsea wadda ta kashe sama da £550m wajen sayo sabbin ‘yan wasa tana da tazarar maki 11 tsakaninta da ta hudu a gasar.

Kenan da kyar za ta buga Gasar zakarun Turai a badi, idan ba ta lashe na bana ba, bayan da ta kasa shiga ‘yan hudun farko kawo yanzu.

A zaman farko da Lampard ya horar a Chelsea ya lashe FA Cup da ya gudanar da aikin.

Lampard – wanda shine kan gaba a ci wa kungiyar kwallaye a lokacin da ya buga wa Chelsea tamaula – ya ci wasa 44 daga 84 a matakin koci.

Daga baya aka doke shi wasa biyar daga takwas a lik, fiye da fafatawa 23 a baya, hakan ya sa ya rasa aikinsa na mai horar da kungiyar Stamford Bridge.

Lampard bai da wata kungiya da yake jan ragama a yanzu haka, tun bayan da Everton ta sallame shi a Janairu, kasa da shekara daya a Goodison Park.

Ranar Asabar Chelsea za ta je Wolverhampton a gasar Firimiya, sannan ta ziyarci Real Madrid a wasan farko a quarter finals a Sifaniya ranar 12 ga watan Afirilu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here