Matasa sun zane basarake, sun kone fadar sa a Taraba

0
430

Wani basarake mai daraja ta uku, Kwe Ando Madugu, wanda ke Karamar Hukumar Ussa ta Jihar Taraba ya sha da kyar a hannun wasu matasa da suka yi masa dukan kawo wuka sannan suka kone fadarsa da motocinsa na hawa.

Bayanai sun nuna matasan sun ji wa basaraken rauni yayin dukan nasa, sannan suka kone fadar tasa da kuma ababen hawan.

Aminiya ta gano cewa matasan sun yi wa fadar basaraken tsinke ne, bayan ya ki amincewa da bukatarsu ta korar wasu makiyaya daga yankin.

Mutanen dai na zargin makiyayan da hannu a kashe-kashe da kuma garkuwa da mutanen da ake fuskanta yankin.

Sun dai zarge shi da hadin baki tare da ba makiyayan mafaka yauin da suke ci gaba da aikata ta’asa a yankin.

Yanzu haka dai basaraken na can kwance a asibiti yana samun kulawar likitoci.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar, SP Usman Abdullahi, ya tabbatar da kai harin kan basaraken, inda ya ce yanzu haka suna ci gaba da zurfafa bincike a kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here