Ko tantance sahihan cibiyoyin cin bashi zai taimaki ‘yan Nijeriya?

0
111

Masana a Nijeriya sun fara tsokaci kan matakin da gwamnatin tarayyya ta dauka na amincewa da cibiyoyin bayar da bashi 173 da su ci gaba da aiki a kasar.

A ranar Talata ne hukumar kare hakkin masu sayen kayayyaki ta Nijeriya FCCPC, ta sanar da wannan umarni bayan da ta shafe lokaci tana tantance cibiyoyin, wadanda a yanzu suke ganiyar tashe wajen yi wa ‘yan kasar tayin karbar bashi akai-akai.

Dakta Isa Abdullahi, mai fashin baki ne kan al’amuran da suka shafi tattalin arziki da kudi, ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa wannan mataki ne mai kyau da zai taimaka wa cibiyoyin ba da bashin da kuma masu karbar bashin.

Masana na ganin gwamnatin ta dauki wannan mataki ne saboda yadda ake yawan samun matsaloli tsakanin cibiyoyin bayar da bashin da mutanen da ke karba.

Kazalika wasu na ganin wani dalilin gwamnati na tantance cibiyoyin shi ne saboda yadda suke yawan “addabar” al’umma wajen aika sakonnin gayyatar karbar bashi akai-akai.

“Wannan mataki ne da ya kamata a ce an dade da daukar sa saboda yadda ake samun matsaloli daban-daban tsakanin masu bayar da bashin da masu karba,” in ji Dakta Isa.

Hukumar ta sha kara wa’adin yi wa cibiyoyin rijista, inda a ranar 27 ga watan Maris ta rufe damar yin hakan gaba daya, ta kuma ce duk cibiyar da ba ta samu amincewa ba to ba za ta ci gaba da wannan aikin a kasar ba.

Dakta Isa, wanda kuma shi ne shugaban sashen koyar da Tsimi da Tanadi na Jami’ar Kashere a Jihar Gomben Nijeriya, ya kara da cewa “bai kamata a ce tun farko an bar wadannan cibiyoyi kara-zube ba, tun da an zo zamanin da hulda da wadannan cibiyoyi ke da muhimmanci.”

Daga cikin cibiyoyi 173 din, 119 ne suka samu cikakkiyar amincewa yayin da 54 suka samu amincewa bisa sharadi, kamar yadda hukumar FCCPC ta wallafa a shafinta na intanet.

Kusan a dukkan kasashen duniya, wadanda suka ci gaba da ma masu tasowa, irin wannan tsari na rancen kudi a kananan cibiyoyi ya zama ruwan dare.

Masana na ganin hakan na faruwa ne sakamakon yadda mutane suka zaku don ganin an samu ci gaba ta fannin tattalin arziki.

“An zo zamanin da kusan kowa yana cin bashi ciki har da gwamnatoci da hukumomi da masana’antu, duk don warware matsaloli da samar da ci gaba da bunkasar jama’a da kasa baki daya,” a cewar Dakta Isa.

Ya kara da cewa ko masu kananan sana’o’i ma suna karbar basussukan nan don inganta harkokinsu, kuma hakan abu ne da zai iya habaka tattalin arzikin kasa.

Matsalolin da ake cin karo da su

Sai dai duk da irin alfanun da karbar bashi daga irin wadannan cibiyoyi na intanet yake da shi, a Nijeriya an sha samun matsaloli a tsakanin bangarorin biyu.

A wasu lokutan irin wadannan cibiyoyi kan ha’inci abokan hulda yayin da sau tari kuma abokan huldar ne ke kin biyan bashin da ake bin su.

Wani ma’aikacin daya daga cikin kamfanonin da gwamnatin ta yarjewa ci gaba da wannan harka, Creditville ya shaida wa TRT Afrika cewa babbar matsalar da suke fuskanta da masu karbar rance ita ce ba sa son mayar musu da kudaden da aka ba su aro.

“Zan iya ce miki kashi 40 cikin 100 na masu karbar bashi ne suka dawo da shi cikin dadin rai, yayin da kashi 20 kuma sai an yi ta musu tuni da bin sawu.

“Amma ragowar kashi 30 din ba sa taba biya, shi kenan kudin sun mula,” in ji ma’aikacin wanda ya nemi a sakaya sunansa.

Matakin da wadannan cibiyoyi ke dauka idan mutum ya ki biya ta dadin rai shi ne sanar da mutanen da suke kut da kut da su, ko kuma sanar da wajen aikinsa.

Idan kuma an buga duk a karshe hakan ya gagara, sai su aika wa hukumar kula da basussuka ta kasa sunan mutum da bayanansa ta yadda za a toshe shi daga samun damar kara cin bashi a ko ina, ko da kuwa a manyan bankuna ne.

“Amma fa sai dai mu hakura da kudin nan don ba za su dawo ba, sun tafi kenan,” in ji ma’aikacin.

A bangaren masu karbar bashin kuma, babbar matsalar da suke cin karo da ita daga cibiyoyin ba da rancen ita ce ta ribar da suke tsauwalawa.

Wani mutum mazaunin birnin tarayya Nijeriya Abuja da shi ma ya nemi a boye sunansa ya shaida wa TRT Afrika cewa ya sha karbar bashin “amma fa gaskiya ribar ta yi yawa,” ya ce.

Ya kara da cewa “Sau tari sai idan mun zo biya mu yi ta fama kuma ga shi ba sa daga kafa, da zarar lokacin biya ya yi ba ka biya ba to za su saka maka tarko ta yadda da kudi sun shiga za su zare nasu.”

Yawanci ribar da wadannan cibiyoyi ke karawa takan kai har kashi 50 cikin 100, kamar yadda wadanda suke karba suka shaida min, kuma masanin tattalin arziki Dakta Isa yana ganin hakan bai dace ba.

“Ribar da suke sakawa ta zarce hankali. Ko manyan bankuna ribar bashinsu ba ta wuce kashi 18 cikin 100. Kananan cibiyoyi irin wadannan bai kamata ribarsu ta wuce kashi 10 cikin 100 ba a gaskiya,” ya ce.

Ya kare matsayarsa da cewa idan kudin ruwa ya yi yawa to talauci na kara samun gindin zama a cikin al’umma da kuma rage walwalar jama’a.

Matakai na gaba

Duk da cewa a bayanin hukumar FECCPC, ta ce ta saki dokoki da sharudda ga cibiyoyin bayar da rancen na intanet don kayyade da sa ido kan yadda suke gudanar da al’amuransu, Dakta Abdullahi na ganin da sauran aikin da ya dace ta yi.

“Ya kamata gwamnati ta tabbatar an bi lungu da sako da amfani da duk wasu kafafen watsa labarai don wayar da kan al’umma su san cibiyoyin da aka yi wa rijista da wadanda ba a yi wa ba.

“Sannan ya zama wajibi a saka wa wadanda aka yi wa rijistar dokoki da sharuuda tare da sa ido don ganin ba su kauce wa ka’idojin ba,” ya jaddada.

A nasa bangaren ma’aikacin cibiyar ba da bashi ta Creditville ma ya ce a yanzu suna daukar matakai don magance “damfarar” da mutane ke musu ta kin biya.

“A yanzu muna rage tsawon lokacin biyan bashin, maimakon shekara biyu ko daya, sai muke mayar da shi ‘yan watannin da ba su wuce shida ba.”

Wani matakin da Dakta Isai ya ce ya kamata su ma cibiyoyin su dauka sun hada da tabbatar da yin rijista da gwamnati da kuma hukumar inshora.

“Hakan zai taimaka wajen rage musu asarar da ake jawo musu. Sannan ka da su dinga ba da bashi sai mutum ya gabatar da wani sahihi da za su kama shi da laifi ko da wanda ya karba din ya tsere.

Kazalika masanin tattalin arzikin ya yi kira ga mutane musamman wadanda ba tsayayyen kasuwanci ko sana’a za su yi da kudin ba da su guji cin bashi haka siddan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here