Bankin duniya ya damu kan yawan bashin da China ke bai wa Afirka

0
116

A wata hira da BBC shugaban Bankin Duniya David Malpass, ya bayyana damuw a kan basukan da China ke dumbuza wa ƙasashen Afirka masu tasowa.

Ya ce kamata ya yi a riƙa bayyana ƙa’idojin yarjejeniyar irin wannan bashi a fili.

”Wannan abin damuwa ne a daidai lokacin da ƙasashe irin su Ghana da Zambiya ke fuskantar matsalar kasa biyan bashi ga ƙasar ta China”, in ji Mista Malpass.

Ita dai, China tana cewa tana ƙulla yarjejeniya da ƙasashen ne bisa tsarin dokokin duniya.

A shekarun baya-bayan na dai, China ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da ke samar da bashi ga ƙasashe masu tasowa.

Wani bincike ya nuna cewa daga 2016 zuwa 2021, China ta ba da rancen dala miliyan 185 ga ƙasashe 22.

Wasu daga cikin cibiyoyin ba da rance na duniya, sun yi zargin cewa China na karɓar kadarorin da ba a yarda da su ba, a matsayin jingina kafin ba da rancen.

Sun kuma yi zargin cewa ƙasashen kan biya rancen a wasu lokuta ta hanyar sayar wa Chinar albarkatun ƙasar da suke da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here