Mesut Ozil ya yi ritaya daga fagen tamola yana da shekaru 34

0
125

Tsohon dan wasan Real Madrid, Arsenal da kuma Jamus, Mesut Ozil ya rataye takalmansa yana da shekaru 34.

Ozil wanda ya lashe kofuna tara, lokacin da yake ganiyar tamola cikin har da kafin FA hudu da kuma La Ligar Spaniya a 2012, ya ce bisa raunikan da yake samu, jikinsa na gaya masa cewar ya kamata ya ajiye takalmansa.

Dan wasan dai ya buga wa kasar sa Jamus wasanni 92, haka zalika ya kasance cikin tawagar da suka ciyo wa Jamus din gasar cin kofin duniya a shekarar 2014.

“Ta kasance tafiya mai ban mamaki da ke cike da lokutan da ba za a manta da su ba,” in ji Ozil a cikin wata sanarwa da ya wallafa a dandalin sada zumunta.

“Na sami damar zama kwararren dan wasan kwallon kafa kusan shekaru 17 a yanzu kuma ina godiya da wannan damar.

Ozil ya fara taka leda a Schalke da Werder Bremen kafin ya koma Real Madrid a 2010, inda ya lashe gasar La Liga da Copa del Rey da kuma Spanish Super Cup.

Ya koma Arsenal ne kan kudin da ya kai sama da Yuro miliyan 42.4 a watan Satumbar 2013, inda ya lashe Kofin FA a kakar wasanni biyu na farko kafin a zabe shi a matsayin gwarzon dan wasa a karo na uku, sannan kuma ya sake lashe kofin a shekarar 2017.

Dan wasan ya zama dan wasan da ya fi karbar albashi a tarihin kungiyar a watan Janairun 2018, inda ya kulla yarjejeniyar shekara uku da rabi kan sama da Yuro 350,000 duk mako, amma ya kasa samun tagomashi a karkashin sabon kocin Arsenal Unai Emery.

Ya koma Fenerbahce a watan Janairun 2021 amma an soke kwantiraginsa bisa wata yarjejeniya a watan Yulin 2022 lokacin da ya koma Istanbul Basaksehir, inda raunin da ya samu ya takaita masa zuwa wasanni takwas da kungiyar ta buga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here