Ramadan: Limaman kirista a Kaduna sun bayar da tallafin abinci ga Musulmai

0
140

Mabiya addinin Islama fiye da dubu guda ne suka karbi tallafin kayakin abinci da kudi daga wata majami’ar mabiyar addinin Kirista a Kaduna a wani yunkurin na tallafa musu gudanar da ibadar azumin watan Ramadana cikin walwala dai dai lokacin da ake fama da tsadar kayakin masarufi.

Miliyoyon mabiya addinin Islama daga sassa daban-daban na duniya ne ke gudanar da azumin ranaku 30 ko 29 a kowacce shekara cikin watan na Ramadana da ke matsayin wata na 9 a kalandar musulunci, azumin da a wannan karon ya zo a wani yanayi na matsin rayuwa da tashin farashin kayaki.

Tawagar limaman majami’ar Evengelical suka jagoranci rabon kayakin abincin da kudi ga mabiya musulmi a babban masallacin jihar Kaduna da ke kan titin zuwa Kano.

Fastor Yohana Buru da ya jagoranci aikin rabon kayan abincin ya bayyana cewa matakin na da nufin kara fahimtar juna da kuma kaunar juna a tsakanin mabiya addinan biyu.

A cewar Buru a halin da ake ciki wajibi ne a hada hannu don taimakon juna lura da karancin takardun kudi a hannun jama’a da ya jefa mutane a wahala baya ga haddasa tsananin tsadar kayakin masarufi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here