Injiniyan Najeriya ya kera motar da za ta iya tashi sama a Borno

0
136

Wani fasihin injiniya a Jihar Borno, Abba Dalori, ya kera tare da hada wata mota da za ta iya tashi sama a jihar.

Abba dai ya kammala karatun digirinsa a Jami’ar Maiduguri, inda ya samu digiri a bangaren Injiniyanci.

Injiniya Dalori ya kwashe shekaru yana kera motar da za ta tashi da kuma tuki a kan hanya kamar yadda ya bayyana.

A cewarsa wannan kirkirar tasa ya yi amfani  ne da wasu abubuwa ma su kamar farfela guda biyu masu karfi ya sa a sama da bayan motar don taimaka mata ta samu ta tashi daga kasa zuwa sama.

Dalori ya ce yana fatan motarsa da ke iya tashi za ta zaburar da sauran matasan Najeriya don ba su kwarin gwiwar ci gaba da sha’awarsu da samar da sabbin hanyoyin ciyar da kasar su gaba wajen kere-kere.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here