Kotu ta gurfanar da wani mahaifi bi sa lalata da ’yar cikinsa

0
142

Yan sanda sun gurfanar da wani mutum mai shekaru 36 a gaban wata kotun majistare da ke Ikeja a Legas ranar Talata bisa zarginsa da lalata da ‘yarsa mai shekaru 18.

Kotun majistare ta bayar da umarnin a tasa keyar mutumin mai suna Roland Okajare a gidan yari bisa laifin da ake zarginsa da shi.

Alkalin kotun, Misis E. Kubeinje, wacce ta mika karar zuwa ga daraktan shigar da kara na jihar Legas (DPP), ta dage sauraron karar zuwa ranar 12 ga Afrilu .

Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, ASP Kehinde Ajayi, ya shaida wa kotun cewa Okajare ya aikata laifin ne a ranar 4 ga watan Janairu, a shagonsa da ke tashar bas ta Ikotun, Legas .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here