Manyan gwamnonin Arewa da zaben gwamna ya yi wa tutsu

0
105

An kammala zaukan shugaban ƙasa da na gwamnoni da kuma ƴan majalisar Dokoki na tarraya da kuma jihohi a fadin Najeriya.

Zaben ya bar wadansu ƴan siyasa cike da murna yayin da wadansu ƴan siyasar suke cike da bakin ciki, saboda yadda sakamakon ya kasance.

A waɗansu jihohin ƙasar an samu sauyi a jam’iyyar da ke mulki inda ƴan adawa suka samu nasara a yayin da a waɗansu kuma masu mulkin ne suka samu dama domin ci gaba da jan ragama.

Bari mu duba jihohi huɗu da suka fi jan hankali, watau Kano da Zamfara da Sokoto da kuma Plateau.

Makomar Ganduje a Kano’

Tun bayan zaben shugaban ƙasa a jihar Kano inda jam’iyyar APC mai mulki ta sha kaye a hannun jam’iyyar adawa ta NNPP, alamu suka nuna cewa gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje sai ya dage idan har yana son ɗan takarar APC, Nasiru Gawuna ya ci zabe.

Amma bayan kammala zaɓen gwamna a ƙarshen mako, sai jam’iyyar NNPP ta kwace ragamar jihar inda hukumar zabe ta ƙasa INEC ta ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Wannan sakamakon ya nuna cewa Ganduje bai kawo jiharsa ba ga jam’iyyar APC a zaben gwamna da kuma na shugaban kasa.

A yanzu ta tabbata cewa a cikin watan Mayu jam’iyyar NNPP ita ce za ta shiga fadar gwamnatin jihar Kano a yayin da APC za ta koma adawa.

Matawalle ya faɗi

Gwamnan jihar Zamfara, Muhammadu Bello Matawalle na jam’iyyar APC ya sha kaye a hannun ɗan takarar jam’iyyar PDP, Dauda Lawal Dare.

Dauda Lawal ya samu kuri’u mafi rinjaye ne a zaɓen kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar.

Jihar Zamfara mai fama da rikicin ƴan bindiga, a yanzu ta koma hannun jam’iyyar PDP.

Dama a shekara ta 2019, kotu ce ta bai wa Matawalle kujerar gwamna bayan da ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar APC ba ta bi ka’ida ba wajen gudanar da zaben fitar da gwani.

Gwamnan jihar Zamfara zai bar kujerarsa a fadar gwamnati da ke Gusau a cikin watan Mayu kuma babu tabbas yadda makomar siyasarsa za ta kasance bayan sauka daga mulki ganin cewa bai samu wa’adin mulki na biyu ba.

Tambuwal a Sokoto

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal zai kammala wa’adinsa na biyu a cikin watan Mayu Sai dai zaben 2023 ya zo masa da rashin tabbas.

Ya yi takarar kujerar sanata a Sokoto amma kuma hukumar INEC ta ce zaben bai kammala ba kuma ba a sa ranar gudanar da cikon zaben ba.

Sai dai kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP da Tambuwal ya tsayar watau Sa’idu Umar ya sha kaye a hannun Ahmed Aliyu na jam’iyyar APC.

Dama dai sakamakon zaben shugaban kasa bai yi wa Tambuwal dadi ba kasancewar Atiku Abubakar na PDP Ya fadi zaben, inda aka bayyana Bola Tinubu na APC a matsayin zababben shugaban Najeriya.

Tambuwal shi ne shugaban kwamitin yakin neman zabe na Atiku Abubakar.

A yanzu abin da ya rage Wa Tambuwal shi ne samun nasara a zaben Sanata kuma akasin haka zai iya jefa makomar siyasarsa cikin ruɗu a yayin da tsohon gwamnan jihar Aliyu Magatakarda Wammako ke cike da murna cewa APC ta lashe zaben gwamnan Sokoto sannan kuma jam’iyyar ce za ta ja ragama a matakin kasa.

Me ya rage Wa Lalong a Plateau ?

Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong na jam’iyyar APC shi ne ya jagoranci yakin neman zabe na jam’iyyarsa a matakin kasa, kuma dan takarar da ya tallata watau Bola Tinubu ya fadi zabe a jiharsa ta Plateau. Amma ya samu nasarar da yawan kuriu a fadin kasar.

Sannan kuma zaben gwamnan jihar bai zo wa Lalong yadda ya so ba saboda jam’iyyar PDP ce ta kwace ragamar jihar daga hannun APC.

A cikin watan Fabarairu ma Gwamna Lalong ya sha kaye a kokarinsa na samun kujerar majalisar Dattijjai inda dan takarar PDP Bali Ninkap Napoleon ya samu nasara a zaben.

Abin zura ido shi ne ko gwamnatin Bola Tinubu za ta tafi tare da Lalong a matakin kasa tun da zai zama dan adawa a jiharsa ta Plateau da ya ja ragama na wa’adin mulki sau biyu.

Sai a ranar 29 ga watan Mayu za a rantsar da sabbin shugabanni a matakin jiha da kuma tarraya a Najeriya kuma fatan duk ɗan siyasa shi ne a dama da shi a cikin gudanar da mulki.

Amma abin da yake a zahiri shi ne cewa wadansu ƴan siyasa ba za su samu abin da suke sa rai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here