Gobara ta tashi a kasuwar Gamboru da ke Maiduguri

0
96

Rahotanni daga Jihar Borno sun nuna a yanzu haka gobara na ci a kasuwar Gamboru da ke Maiduguri, babban birnin jihar.

Kasuwar Gamboru ita ce kasuwa ta biyu mafi girma a Maiduguri, bayan Kasuwar Monday, wadda ta yi gobara, mako uku da suka gabata.

Gobarar na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu rahoton wata gobara a Babbar Kasuwar Biu da ke jihar.

Kowace daga cikinsu ta tashi ne a yayin da jama’a da kada kuri’a a zaben gwamnoni da ’yan majalisar dokokin jiha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here