Jihohin da za a iya samun matsala a sakamakon zaɓen gwamnoni – CDD

0
81

Wani rahoto ya ce taɓarɓarewar tsaro a sassa da dama, da yiwuwar hargitsa zaɓe, na iya zama illolin da za su shafi sahihancin zaɓen gwamnoni, da kuma yiwuwar samun sakamakon da bai kammala ba, ranar Asabar a Nijeriya.

Hakan a cewar rahoton na Cibiyar Bunƙasa Dimokraɗiyya da Raya Ƙasa (CDD), na iya yin tasiri ga niyyar ‘yan ƙasar na fita su yi zaɓe, baya ga ƙarancin man fetur da takardun naira da ake ci gaba da fama da su.

Duk da yadda sakamako ya kaya, rahoton ya ce za a zaɓi sabbin gwamnoni a jiha 17, sai jiha 11 inda gwamnoni masu ci ke neman wa’adi na biyu.

Ban da zaɓukan gwamnoni guda 28, za kuma a yi zaɓen ‘yan majalisun dokokin jihohi a duk faɗin Nijeriya.

CDD ta ce sahihan zaɓuka, muhimmin abu ne, amma zaɓen na ranar Asabar, 18 ga watan Maris, zai gamu da ƙalubale kamar na barazanar tayar da rikici da cikas wajen kai kaya da ma’aikatan zaɓe, saboda matsalolin tsaro da ƙarancin takardun kuɗi da na man fetur, akwai kuma raguwar amanna ga Hukumar zaɓe saboda rashin fara zaɓe kan lokaci da tangarɗar na’ura da suka baibaye zaɓukan shugaban ƙasa da na majalisar dokokin tarayya da ya gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here