Shin da gaske ne wannan amaryar bazawara ce?

0
134

A wanann makon ne soshiyal mediya ta dau zafi sakamakon bullar bidiyon wani dattijon Ango ya na budar kan matashiyar amaryarsa.

Nan take ’yan gaza-gani da ’yan bani-na-iya suka ce wuuuu wannan ’ya ta yi kankanta da aure, kuma in ma ta isa, ba dai da wannan ‘kakan na ta’ ba.

Wannan dai ba ya rasa nasaba da karamar kira da take da ita, da har wasu ke kallon ba ta wuce shekaru 12 ba.

Sai dai binciken Aminiya ya gano cewa amarya mai suna Sakina Musa Waziri dai bazawara ce mai shekaru akalla 21.

Kuma angonta da aka gan su cikin bidiyo shi ne Dan Malikin Bauchi, Alhaji Aminu Muhammad.

Sakina dai haifaffiyar Unguwar Railway ce da ke Birnin Bauchi.

Mahaifinta Malam Musa Waziri tsohon alkali ne.

Ta kuma shiga Jami’ar jihar Bauchi da ke Gadau kafin ta yi auren fari. Sai dai auren bai dade ba suka rabu.

A nan Allah Ya haɗa ta da Dan Maliki har aka sha biki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here