Rundunar MNJTF ta kama mayakan ISWAP da dama a yankin tafkin Chadi

0
94

Rundunar hadin gwiwa ta Multi national Joint Task Force MNJTF ta ce dakarunta na Sashe na 3 da na 4 sun kama sama da mutane 900 da ake zargin ‘yan uwa ne da ke aikin hadin gwiwa da mayakan Boko Haram ko kuma ISWAP.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin rundunar a birnin N’Djamena da ke kasar Chad, wato Laftanal KanaKamarudeen Adegoke, ya fitar.

Adegoke ya ce fadan da kungiyoyin ‘yan ta’adda na Boko Haram da ISWAP ke yi, da kuma matsin da rundunar MNJTF da sauran hare-haren bama-bamai daga dakarun gwamnati, musamman hare-haren ta sama ne ya tilastawa mayakan mika wuya.

Ya bayyana cewa an ci gaba da kwashe dimbin jama’a daga dazukan Sambisa zuwa tafkin Chadi a cikin wata daya da ya gabata.

Kazalika, sojojin runduna ta 4 sun gudanar da sintiri na dare a Ngagam Djalori inda suka ceto mata uku tare da ‘ya’yansu hudu da ke tserewa fadan da ake yi tsakanin ‘yan Boko Haram da ISWAP daga dajin Sambisa.

Ya ce hakan ya biyo bayan kama wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne da ke samar da kayan aiki a lokacin da suke kokarin fita daga garin Munguno zuwa Tumbun domin mika makamai ga ‘yan ta’addan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here