EFCC ta damke ‘yan damfara 21 a Abuja

0
96

Hukumar Yaki Da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta kama wasu mutane 21 da ake zargi da damfara yanar gizo.

Wadanda ake zargin wadanda aka kama a ranar Talata sun hada da Joseph Boniface da Emmaneul Okwara da Elijah Iwebie da Moses Hassan da Abdulrahman Lawal da Azu Chidubem Eugene da Abdullahi Adebola da kuma Elijah Simon.

Sauran sun hada da Terfa Lincoln, David Kome, Chukwudah Martinez, Adie Matthew, Canice Agabi, Abbas Aminu, Damilare James da Christopher Simon.

Wadanda aka kama sun hada da Mohammed Abdulhamid, Ifeanyi Bosah, Ayuba Aminu, Godwin Terkura da kuma Victor Ademola.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter ta ce an kama wadanda ake zargin ne a unguwar Lugbe da Kubwa a Abuja.

Kamen nasu ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu kan ayyukan damfara da ake zarginsu da aikatawa ta Intanet.

Wasu daga cikin kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da kwamfutoci uku, mota kirar Mercedes CLA250, manyan wayoyin hannu guda 25 da kuma mota kirar C300.

EFCC ta kara da cewa za ta gurfanar da su a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here