Buhari ne mafi munin shugaba da Najeriya ta gani a tarihi – Hanga

0
115

Zababben sanatan da zai wakilci Kano ta tsakiya a Majalisar dattawan Najeriya Rufa’i Hanga, ya bayyana gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mafi muni da kasar ta taba gani a tarihi.

A lokacin wata ganawa da ya yi da kafar Talabijin ta Trust TV, Rufa’i Hanga da ya yi shura wajen tallata siyasar shugaban Muhammadu Buhari a jihar Kano tsawon shekaru, ya ce shugaban ya gaza kuma bashi da nagartar jagoranci.

A cewar zababben sanatan na Kano ta tsakiya, Buhari bai can-canci a rinka kiran sa da sunan ”Mai Gasiya ba”, ganin yadda ya ke kewaye da mutanen da ke fuskantar tuhuma a wajen hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriyar EFCC.

Sanata Hanga ya ce babu wani shugaba da zai gudanar da salon mulkin Buhari ya kuma yi ikirarin shi ya fi kowane shugaba gudanar da aiki a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here