A kalla mabaratan Nijar dari 580 hukomomin kasar suka mayar gida

0
103

Daruruwan ‘yan jamhuriyar Nijar da ke yawon bara a titunan birnin Dakar na kasar Senegal, wadanda aka bayyana halin da su ke ciki a wani shirin talabijin aka maida su kasarsu a daren Juma’a zuwa Asabar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito wakilinsa na cewa.

Jirgin da ya kwaso mabaratan 580, wanda gwamnatin Nijar ce ta yi hayarsa ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Yamai da karfe 1 da minti 20 agogon Nijar da Najeriya.

Jim kadan bayan saukar mabaratan a Yamai, ministan cikin gidan Nijar, Hamadou Adamou Souley ya ce gwamnatin kasar sa ta dau wannan mataki ne duba da yadda barar da su ke yi, ya ke bata sunan Nijar a idon duniya.

A makon da ya wuce ne tashar talabijin din Senegal ta TFM ta yada irin zaman kaskancin da wadannan mabarata ‘yan kasar Nijar ke yi a babban birnin kasar Dakar, lamarin da ya harzuka mahukuntan Nijar dama daidaikun al’ummar kasar da ke kallon matakin a matsayin cin mutunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here