Majalisar dinkin duniya ta ware ranar yaki da kyamar addinin Musulunci ta duniya

0
132

Majalisar dinkin duniya ta gudanar da bikin ranar yaki da kyamar addinin Musulunci karon farko a tarihi. An dai gudanar da gagarumin biki a babban dakin taro dake shalkwatar majalisar dinkin duniyar da ke New York ta Amurka

Kamar dai yadda fassara ke nunawa, Kyamar addinin Musulunci na nuna jin tsoron Mabiya addinin ko nuna musu wariya ko kuma fargabar cutarwa daga gare su ko kuma alakanta su da ta’addanci. 

Manema labaran da suka halarci gagarumin bikin sun ruwaito masu jawabi yayin taron na bukatar a yi gaggawar bijiro da dokoki masu tsauri ga masu kyamar addinin Musulunci ko musulmai, mafi muhimmanci kuma shine a dakatar da al’adar alakanta musulun ci da ta’addanci.

Tun a watan Maris din 2022 ne majalisar dinkin duniyar ta ayyana ware ranar 11 ga watan Maris din kowacce shekara a matsayin ranar yaki da kyamar addinin Musulunci bayan wani tattakli da kungiyoyin kare hakkin dan adam da na addinai suka yi zuwa majalisar da nufin janyo hankalin ta kan daukar mataki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here