Wasu matasa sun yi wa kurma mai shekara 15 fyade

0
123

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da yi wa wata yarinya kurma mai shekara 15 fyade da karfin tsiya.

Kakakin rundunar a jihar, DSP Ramhan Nansel ne ya tabbatar da kamen a cikin wata sanarwa ranar Juma’a.

Ya ce wadanda ake zargin sun yi amfani da kasancewar yarinyar kurma wajen aikata mata fyaden.

Ramhan ya ce, “A ranar biyu ga watan Maris, 2023, da misalin karfe 6:30, an kawo mana kara a ofishin rundunarmu da ke Karamar Hukumar Obi, cewa wani mai suna Aminu Hashim mai shekara 24 da kuma wani Lukman Dogara, mai shekara 18, mazauna titin Owolosho da ke Karamar Hukumar Obi ta Jihar Nasarawa, sun hada baki wajen yi wa yarinya mai shekara 15 fyade.

Bayan samun korafin, sai jami’anmu na yankin suka dukufa bincike da farautar wadanda ake zargi da aika-aikar.

“Binciken farkeo-farko ya nuna cewa wadanda ake zargin sun yaudare rarinyar wacce take da larurar ji zuwa gidansu da ke kan layin Okpe a Karamar Hukumar Obi, inda suka yi mata fyaden.”

Kakakin ’yan sandan ya kuma ce nan take aka garzaya da wacce aka yi wa fyaden zuwa asibit domin a duba lafiyarta.

Ya ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Maiyaki Baba, ya bayar da umarnin zurfafa bincike a kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here