Kotu ta tsare tsohon mataimakin gwamnan a kurkuku

0
119

Kotun Majastare mai zamanta a Owerri, babban birnin Jihar Imo, ta tisa keyar tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Imo, Gerald Irona, zuwa gidan yari.

A ranar Laraba ’yan sanda a jihar suka cafke Irona kan zargin aikata ba daidai ba.

Bayan sauraren lauyoyin bangarorin biyu, alkalin kotun, C.N Ezerioha, ya ba da umarnin a tsare shi a gidan yarin Owerri kan zargin furucin da bai dace ba.

A cewar ’yan sanda, furucin da Irona ya yi a Kotun Koli yayin shari’a tsakanin Gwamna Hope Uzodimma da tsohon Gwamnan Jihar, Emeka Ihedioha, shi ya jawo masa matsala aka kama shi.

Alkalin ya ba da umarnin tsare Irona ne saboda hurumin sauraren karar da ya ce kotun ba ta da shi.

Lauyansa, S.I Imo, ya bukaci kotun ta ba da belin wanda yake karewa.

Sai dai lauyan mai kara, Sunday Ogbuji, ya ki yarda da belin da takwaransa ya nema, yana mai cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar.

Ogbuji ya ce Babbabr Kotu kadai ke da hurumin ba da belin wanda ake zargi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here