INEC ta dage zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha

0
115
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dage zaben gwamnoni da na yan majalisun jihohi na shekara ta 2023, da aka shirya gudanarwa ranar Asabar 11 ga Maris, 2023 zuwa 18 ga Maris, 2023.
Daily trust ta rawaito Rahotanni sun ce har yanzu INEC ba ta sake fasalin tsarin tabbatar da na’urar BVAS ba, wadda ta haifar da matsaloli a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan fabarairun 2023.
 Idan dai ba a manta ba a safiyar yau ne kotun kolin Najeriya ta ba hukumar umarnin sake fasalin tsarin BVAS, a shirye-shiryen gudanar da zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki na jihohi a Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here