‘Yan bindiga sun kone gidaje tare da hallaka mutane fiye da 50 a Kwande

0
114

Tun ranar da aka gudanar da zaben shugaban kasa da ‘yan majalisu ne, mahara suka fara kasha-kashe da kone-konen gidaje da dukiyoyi, yayinda wassu mutane da dama suka sami raunuka.

Shugaban kungiyar kabilar Tivi na kasa da kasa, Chief Iorbee Ihagh, tsohon kwamishinan ‘yan sanda, ya ce rikicin ya faro ne tun shekaru takwas da suka gabata.

‘’Ya ce makiyaya sun zo sun tarwatsa mutane, suka lalata duk makarantu da gwamnati ta gina da asibitoci, majami’u da dukkan gine-gine ciki har da gidajena guda uku, sun kore mu daga garuruwanmu, yanzu haka akwai ‘yan gudun hijira a ko’ina.’’

Chief Iorbee yace ‘’ a kwanan nan sun kashe mutane hamsin, nine ma na kai rahoto wa jami’an tsaro da gwamnati da sarakuna, kafin aka tura sojoji, kwanaki biyu da suka gabata.’’

Ya ce ‘’yanzu haka mutane sun tarwatse, ba abinci, yaransu basa zuwa makaranta, basu da wurin kwana, akwai ‘yan gudun hijira fiye da miliyan biyu a Jahar Binuwai.’’

Ko me kuke yi don samun zaman lafiya?

Ya ce ‘’kamata yayi mu sami hadin kai, maimakon mu kasance a rabe, hakan baya taimakonmu, amma dole mu bi doka da gwamnatin Jahar Binuwai ta sanya na hana kiwo a sarari, wanda dukkan masu ruwa da tsaki suka amince, don me makiyaya ba zasu bi dokar ba, don kauce wa barnata dukiyoyin manoma?’’

Shugaban na kabilar Tivi ya ce zai ci gaba da magana da mutanensa, amma dole sai gwamnatin tarayya ta taimaka musu.

A gefe guda kuwa, shugaban kungiyar Miyetti Allah a Jahar Binuwai, Ardo Risku Muhammed ya ce babu Fulani a wurin da ake rikicin, don haka ba Fulani ne suka aika ta’asar ba.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jahar Binuwai, Kate Anene Sewuese ta ce bata da cikakken bayani kan abinda ya faru, idan ta samu zata tuntube ni, sai dai har na hada wannan rahoto, ban sami kira ko sako daga gareta ba. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here