Wani soja ya hallaka kwamandan sa da wasu sojoji 2 daga bisani ya harbe kan sa a Sokoto

0
107

Wani sojan Najeriya ya dauki bindiga ya kashe Kwamandan sa, da wasu sojoji biyu daga baya ya kashe kan sa da kan sa a sansanin ‘Forward Operating Base’, Rabah da ke jahar Sokoto.

Sojan da aka gano shi da Lance Corporal Nwobobo Chinoso yana aiki a karkashin bataliya ta 223 da ke Zuru ta jahar Kebbi, an kuma tura shi aiki sansanin Forward Operating Base Rabah, kana lamarin ya faru ne a gidan Kwamandan sansanin a ranar Lahadi.

Ya bude wuta inda ya kashe Kwamandan FOB, Lt. T.I. Sam-Oladapo, da wasu sojoji biyu ciki har da Sajen Manjo (CSM), Iliyasu Inusa da Private Attahiru Mohammed, daga bisani ya juya bindigar zuwa kansa kuma shi ma haka ya mutu.

A wani bayanin, faruwar lamarin da LEADERSHIP ta ci karo da shi, ya yi nuni da cewa hatsarin ya faru ne a ranar Lahadi 5 ga watan Maris na 2023 wajajen karfe 5 na yamma, sannan har zuwa yanzu ba a iya gano musabbabin bude wutar ba, amma an kaddamar da bincike kan lamarin.

An ce Kwamandan runduna ta 8 Garrison da Kwamandan bataliya 26 sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, ana kan kokarin kwasan gawarwakin zuwa dakin adana gawarwaki na asibitin koyarwa ta jami’ar Usman Danfodio (UDUTH) da ke Sokoto.

An yi kokarin jin ta bakin daraktan sashin yada labarai na rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar, Onyema Nwachukwu, amma haka ba ta cimma ruwa ba, sai dai wasu majiyoyin soja sun tabbatar wa LEADERSHIP da faruwar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here