’Yan bindiga sun sace iyalan sarki a Taraba

0
111

’Yan bindiga sun yi awon gaba da iyalan Sarkin Kudu, Dansalama Adamu da ke Karamar Hukumar Ibbi a Jihar Taraba.

Lamarin kamar yadda Aminiya ta ruwaito ya faru ne a ranar Alhamis, inda masu garkuwa don neman kudin fansa suka sace matan Sarkin biyu da dansa daya.

Bayanai sun nuna cewa al’ummomin yankin suna zaune cikin zulumi kan yadda a kwanakin nan barayin mutanen suka addabe su.

Rahotanni sun ce a ranar Alhamis da daddare ne aka shiga garin aka sace iyalan Sarkin mai daraja ta uku kuma har yanzu babu labarinsu.

Mutanen yankin na Sarkin Kudu sun ce a yanzu ba sa samun yin barci cikin kwanciyar hankali saboda karuwar ta’addancin masu garkuwa da mutanen.

Wani daga cikin makusantan sarkin garin ya yi bayanin cewa, a ranar Alhamis barayin suka je gidan sarkin da nufin sace shi, amma ba su samu sa’a ba, sai suka yi gaba da matansa biyu.

Ya kara da cewa wannan matsala ta yi kamari shekara biyu da ta gabata a yankin nasu, amma sakamakon tsauraran matakai da gwamnatin jiha da ta Karamar Hukuma da sauran jam’ian tsaro suka dauka sai ta lafa.

“Amma kuma yanzu abin ya sake dawowa inda a sati biyu ko uku da ya gabata an saci wani yaro, an dawo da shi aka kuma sake daukar wani wanda ba a dawo da shi ba har yanzu.”

Ita ma wata mata da masu garkuwa da mutanen suka sace ’ya’yanta biyu ta ce suna cikin wani hali na tashin hankali saboda ayyukan mutanen.

Ta bayyana cewa bayan da suka saci danta daya, an biya kudin fansa sun sako shi sai kuma suka kara sace daya, wanda har yanzu ba su sako shi ba, suna neman a ba su Naira miliyan 20 kafin su sako shi.

Bayanai sun ce ya zuwa yanzu jami’an tsaro da ‘yan sa-kai na cikin daji sun bi sawun mutanen a kokarin da suke yi na ganin sun kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su.

Aminiya ta tuntubi mai magana da yawun ‘yan sandan jihar ta Taraba, SP Usman Abdullahi, inda ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa an cafke wasu ababen zargi.

Jihar Taraba dai na cikin jihohi da ke fama da matsalar masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa musamman ma a yankin Kudancin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here