Zaben shugaban kasa: Atiku ya lashe Bayelsa

0
109

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya lashe Jihar Bayelsa.

Atiku dai ya sami nasarar ce bayan ya doke Bola Tinubu na APC da kuma Peter Obi na LP.

Jami’in tattara sakamakon zabe a Jihar, kuma Shugaban Jami’ar Benin, Farfesa Lilian Salami ne ya sanar da sakamakon zaben a Yenagoa, babban birnin Jihar ranar Litinin.

Ya ce Atiku ya sami kuri’a 68,818, yayin da Peter Obi na LP ya sami kuri’a 49,975.

Sakamakon ya kuma nuna Bola Ahmed Tinubu na APC ya sami kuri’a 42,572, inda ya zo na uku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here