Peter Obi ya kayar da Tinubu da Atiku a Abuja

0
110

Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi, ya lashe zaben da aka gudanar Abuja, Birnin Tarayya, da tazara mai yawa.

Peter Obi ya samu kuri’u 281,667 daga kananan hukumomi shida da ke Abuja, a yayin da Bola Tinubu na Jam’iyyar APC ya zo na biyu da kuri’a 90,902, sai Atiku Abubakar na PDP wanda ya samu kuri’u 73,743 a matsayin na uku.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here