Ganduje ya yi rashin nasara a hannun kwankwaso a karamar hukumar Tofa

0
108

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya rasa kawo karamar hukumar sa ta Tofa da ke jihar yayin zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisu da ya gudana a asabar din da ta gabata.

Sakamakon zaben dai ya nuna cewa Jam’iyyar NNPP da tsohon gwamnan jihar Rabi’u Musa Kwankwaso ke jagoranta ce ta lashe zaben karamar hukumar da gagarumin rinjaye tsakaninta da APC.

Gwamnan jihar ta Kano wanda ya dan asalin kauyen Ganduje ne da ke karamar hukumar Tofa, wannan ne karon farko da ya rasa damar iya kawo karamar hukumar tasa wadda ta fada hannun babban abokin adawarsa Rabi’u Musa Kwankwaso.

Sakamakon Zaben karamar hukumar ta Tofa na nuni da cewa Jam’iyyar NNPP ta Kwankwaso ke kan gaba da kuri’u dubu 25 da 072 yayinda APC ke da kuri’u dubu 16 da 773.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here