‘Yan Najeriya na ci gaba da dakon sunan wanda zai maye gurbin shugaba Buhari

0
124

Ana ci gaba da kidayar kuri’u a Najeriya, kwana guda bayan gudanar da zabe mai cike da tarihi a tsakanin ‘yan takara uku da ke fafatawa a zaben shugaban kasa mafi yawan al’umma a Afirka.

Kusan masu kada kuri’a miliyan 90 ne suka fito zaben na ranar Asabar, wanda aka gudanar da shi cikin lumana, duk da cewa tashe-tashen hankula, jinkiri da kuma cikas na fasaha sun sa mutane da dama zaman jira har zuwa dare domin kada kuri’a wasu sassan kasar.

Bayan wa’adi biyu na Shugaba Muhammadu Buhari, ‘yan Najeriya da dama na fatan sabon shugaba zai iya yin aiki mai kyau wajen magance matsalar rashin tsaro da rashin aikin yi da kuma magance talauci da ke addabar al’ummarsu.

Daga cikin manyan ’yan takarar da suka fafata a zaben, hudu sun yi fice: Bola Ahmed Tinubu, daga APC, Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar adawa (PDP), da Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP, sai kuma Peter Obi, wanda jam’iyyar Labour ke marawa baya.

Matsalar rashin tsaro dai wani babban batu ne na yakin neman zabe, inda Najeriya ta yi fama da rikicin masu tayar da kayar baya na tsawon shekaru 14 a yankin arewa maso gabas wanda ya raba mutane miliyan 2 da muhallansu, da kuma ‘yan bindiga a yankin arewa maso yamma sai kuma rikicin ‘yan awaren yankin kudu maso gabas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here