Obasanjo ya sha kaye a hannun Tinubu a rumfar zabensa

0
146

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ya sha kaye a rumfar zabe ta tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na 2023.

In za ku iya tuna cewa tsohon shugaban kasar ya na marawa  Obi baya a matsayin dan takarar da ya fi so gabanin zaben shugaban kasa.

Jim kadan bayan kidaya kuri’u a mazabar Obasanjo da ke Ward 11, Unit 22, a karamar hukumar Abeokuta ta Arewa a jihar Ogun, dan takarar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya samu kuri’u 56 ya kayar da Obi.

Idan aka yi la’akari da yadda aka yi zaben, Obi ya samu kuri’u 9, sannan dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya samu 7, yayin da Tinubu ya samu kuri’u 56 a matsayin mafi yawan kuri’u.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here