Gwamnatin tarayya ta rufe iyakokin kasa don zaben shugaban kasa

0
104

Gabanin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a yi ranar Asabar, gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin rufe dukkan iyakokin kasar baki daya.

Ya ce za a rufe iyakokin daga ranar Asabar zuwa Lahadi.

Sanarwar ta ce; Gwamnatin tarayya ta bada umarnin rufe dukkan iyakokin kasa daga karfe 00:00 na ranar Asabar 25 ga Fabrairu 2023 zuwa karfe 00:00 na rana Lahadi, 26 ga Fabrairu, 2023.

“Saboda haka, duk Kwamandan Kwamandojin musamman na Jihohin kan iyaka su tabbatar da aiwatar da wannan umarni sosai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here