Gwamnatin tarayya ta tabbatar hare haren Amurka a jihar Sokoto

0
13

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa Najeriya na ci gaba da yin tsayayyen haɗin gwiwar tsaro da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, domin tinkarar barazanar ta’addanci da rikice-rikicen tsaro, biyo bayan rahotannin kai hare-haren sama kan wuraren ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma na ƙasar nan.

A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta fitar a safiyar Juma’a, ta bayyana cewa hare-haren sun samo asali ne daga haɗin kai na musayar bayanan sirri da tsara dabarun tsaro tsakanin hukumomin tsaron Najeriya da abokan hulɗar ta na ƙasa da ƙasa.

 Sanarwar ta ce irin wannan haɗin gwiwa na bin ka’idojin da duniya ta amince da su wajen yaƙi da ta’addanci.

Ma’aikatar ta jaddada cewa duk wani aikin tsaro da ake aiwatarwa yana gudana ne cikin mutunta ikon ƙasar Najeriya, tare da bin dokokin ƙasa da ƙasa da yarjejeniyoyin diflomasiyya da aka kulla tsakanin ƙasashen da abin ya shafa. Ta ƙara da cewa hare-haren sun yi daidai da manufofin kare ƙasa da rayukan al’umma daga hare haren ƴan ta’adda.

Sanarwar ta nanata cewa kariyar fararen hula ita ce ginshiƙin dukkan ayyukan yaƙi da ta’addanci a Najeriya. Gwamnati ta ce tana da aniyar kare rayuka, tabbatar da haɗin kan ƙasa, da kuma mutunta haƙƙi da mutuncin ‘yan ƙasa ba tare da la’akari da bambancin addini ko ƙabila ba.

Haka kuma, Ma’aikatar ta bayyana cewa duk wani nau’i na ta’addanci, ko ana kai shi kan Musulmi, Kiristoci ko wasu al’umma, abin Allah wadai ne, kuma babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaro a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

Ma’aikatar Harkokin Wajen ta ƙara da cewa Najeriya na ci gaba da aiki kafada da kafada da abokan hulɗar ta domin raunana ƙungiyoyin ‘yan ta’adda, katse hanyoyin samun kuɗi, makamai da kayan aiki, da kuma hana barazanar da ke ketare iyakokin ƙasa.

A ƙarshe, gwamnatin ta ce za ta ci gaba da sanar da jama’a duk wani sabon bayani ta hanyoyin hukuma, yayin da take ƙara ƙarfafa tsare-tsaren tsaro domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa a faɗin ƙasar nan.

A cikin daren Juma’a ne shugaban Amurka Donald Trump, ya wallafa cewa sojojin kasar sa, sun yi luguden wuta a kan maɓoyar ƴan ta’addan ISIS a jihar Sokoto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here